Kungiyar Kwankwasiyya ta musanta rahotannin da ke cewa jagoranta, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) saboda rikici kan batun sauya sunayen ‘yan takara.
A cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Habibu Mohammed, ya fitar, Kwankwasiyya ta ce rahoton ƙarya ne kuma ba shi da tushe, tana mai tabbatar da cewa Kwankwaso bai bayyana niyyar barin jam’iyyar ba.
Kungiyar ta ce ko Kwankwaso ko ita kanta Kwankwasiyya ba su koka kan sauya wasu daga cikin ‘yan takarar da aka gabatar ba, sabanin jita-jitar da ke yawo a kafafen siyasa.
Rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar kungiyar ta fice daga NDC bayan sauya sunayen wasu ‘yan takarar da ta gabatar, abin da ake zargin ya sabawa yarjejeniyar raba mulki a cikin jam’iyyar.
Sai dai kakakin ya bayyana cewa an gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar 29 ga Mayu bisa ka’idojin dokar zabe da jagororin INEC, kuma an tabbatar da sakamakon zaben.
Ya kara da cewa shugabannin jam’iyya sun riga sun amince da tsarin amincewa da dan takara daya (consensus) a wasu wurare, kuma an mika jerin sunayen da aka amince da su ba tare da wata rigima ba.
Kwankwasiyya ta kuma ce Kwankwaso bai kai wata korafi a hukumance ga jam’iyyar ba, tana mai kiran rahotannin da ke yawo da cewa jita-jita ce kawai.

0 $type={blogger}:
Post a Comment