Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da mutuwar mutane hudu sannan 24 suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin kasa da ya faru a layin jirgin ƙasa na Warri–Itakpe kusa da Agbor a Jihar Delta.
Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa wasu taragon jirgin guda hudu sun kife yayin da wani ya kauce daga layin dogo a lokacin hatsarin da ya faru a ranar Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa jimillar mutane 482 ne ke cikin jirgin, ciki har da fasinjoji 442, da kuma ma’aikata da jami’an tsaro da masu bada hidima 40.
An tura jami’an agaji da suka hada da NEMA da FRSC da ‘yan sanda da hukumar tsaron farin kaya na gwamnatin jihar Delta zuwa wajen domin gudanar da aikin ceto.
Bayan kammala aikin ceto daga baya, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitoci a Agbor domin kula da su.
Ma’aikatar Sufuri ta tabbatar da cewa daya daga cikin ma’aikatan NRC ya samu mummunan rauni a hannu, amma yana cikin kwanciyar hankali.
Hukumomi sun mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da jinjinawa jami’an agaji bisa gaggawar da suka yi wajen kai dauki.
An kuma fara bincike domin gano dalilin hatsarin, yayin da ake ci gaba da tantance sunayen wadanda abin ya shafa domin ba su taimako da tallafi.

0 $type={blogger}:
Post a Comment