Adadin wadanda Suka Mutu a Girgizar Ƙasar Philippines Ya Kai Mutane 37, Yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Adadin wadanda Suka Mutu a Girgizar Ƙasar Philippines Ya Kai Mutane 37, Yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Akalla mutane 37 ne suka rasa rayukansu sannan kusan 400 suka jikkata bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta kai maki 7.8 ta afku a kudancin Philippines, yayin da jami’an agaji ke ci gaba da aikin ceto cikin gaggawa.

Mafi yawan barnar ta faru ne a birnin General Santos da ke tsibirin Mindanao, inda gine-gine da dama suka rushe tare da binne mutane a ƙarƙashin baraguzai. 
Ma’aikatan agaji na ci gaba da aikin tono domin gano waɗanda suka makale, yayin da aka tabbatar cewa mutane biyu har yanzu ba a gano su ba a wani ginin kasuwa.

Hukumomi sun bayyana cewa an samu girgizar ƙasa bayan girgizar farko, ciki har da wata girgiza mai karfin maki 6.5, wacce ta ƙara dagula aikin ceton. 
Girgizar ta kuma shafi yankuna da dama, inda aka fitar da gargaɗin tsunami na ɗan lokaci a wasu wurare kusa.

An ayyana dokar gaggawa a General Santos saboda lalacewar gine-gine da hanyoyi da suka toshe, da kuma katsewar wutar lantarki da ke hana aikin agaji tafiya cikin sauƙi. 
Har ila yau, zaftarewar ƙasa a wasu larduna ta ƙara yawan waɗanda suka mutu.

Jami’ai sun yi gargadin cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da aikin ceto a wuraren da ke da wahalar isa.

0 $type={blogger}: