Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Amurka Ta Amince Trump Ya Ci Gaba da Tsarin Korar Baƙi Cikin Gaggawa.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Amurka Ta Amince Trump Ya Ci Gaba da Tsarin Korar Baƙi Cikin Gaggawa.

Wata kotun ɗaukaka ƙara a ƙasar Amurka ta yanke hukuncin cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump za ta iya ci gaba da faɗaɗa tsarin korar baƙi daga ƙasar cikin gaggawa.

Kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Gundumar Columbia ya soke wani hukunci na baya da ya dakatar da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) daga faɗaɗa amfani da tsarin korar cikin gaggawa.

Wannan hukunci ya zama babban nasara ga manufofin gwamnatin Trump na tsaurara matakan shige da fice da kuma shirin korar bakin da yawa daga ƙasar.

A baya, ana amfani da tsarin korar cikin gaggawa ne musamman ga baƙin da aka kama a kan iyakar Amurka. Amma gwamnatin Trump ta nemi faɗaɗa shi domin ya shafi baƙin da aka kama a ko’ina a cikin Amurka, idan ba za su iya tabbatar da cewa sun shafe sama da shekaru biyu a ƙasar ba.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun yi adawa da wannan mataki, suna cewa yana iya take haƙƙin baƙi na samun damar gabatar da hujja a gaban doka kafin a kore su.

Ƙungiyar kare haƙƙin baƙi ta Make the Road New York ce ta shigar da ƙarar. Wata kotun ƙasa ta baya ta ce tsarin na iya jawo kurakurai tare da sa a kori mutanen da bai kamata a kore su ba.

Sai dai kotun ɗaukaka ƙarar ta sauya wannan hukunci, inda Alkali Justin Walker ya ce gwamnati na iya amfani da tsarin korar cikin gaggawa “gwargwadon iyakar da Majalisa ta amince.”

0 $type={blogger}: