Kotu Ta Yankewa Mahaifiyar Dan Fashin Daji Da ’Yar’uwarsa Hukuncin Shekaru 40 a Gidan Yari Saboda Taimakawa Ta’addanci.

Kotu Ta Yankewa Mahaifiyar Dan Fashin Daji Da ’Yar’uwarsa Hukuncin Shekaru 40 a Gidan Yari Saboda Taimakawa Ta’addanci.

Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mahaifiyar wani fitaccen shugaban ’yan ta’adda da aka kashe, Ibrahim Battujo, da kuma ’yar’uwarsa hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari kowacce, bisa zargin taimaka masa wajen ayyukan ta’addanci.

Mai shari’a Hauwa Yilwa ta yanke hukuncin ne bayan Safiya Salihu da Halima Abdullahi sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su da suka shafi ta’addanci, wanda Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya shigar.

Sojojin Najeriya sun kashe Battujo a ranar 10 ga Yuni, 2026, bayan wani yunkurin sace dalibai da kai hari kan masu rubuta jarabawar WAEC a wani daji da ke kusa da Iluke, karamar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi.

Kotun ta same su da laifin taimakawa da goyon bayan ayyukan Battujo ta hanyar isar masa da bayanai ta wayar tarho, wanda ya sabawa dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022.

An kuma samu mahaifiyar tasa da laifin boye bayanai game da ayyukan danta bayan ta ziyarce shi a sansaninsa na daji kuma ta gan shi da makamai.

Ita kuma ’yar’uwarsa an same ta da laifin boye bayanan da ka iya taimakawa wajen cafke shi.

Kotun ta umurci cewa hukuncin zai gudana ne lokaci guda, kuma bayan kammala zaman gidan yarin za a yi musu shirin gyara hali.

0 $type={blogger}: