Jami'ar tarayya ta Oye-Ekiti (FUOYE) Ta Dakatar Da Dalibai Biyu Kan Zargin Yada Bidiyon tsiraici Na Shugaban Daliban jami'ar.

Jami'ar tarayya ta Oye-Ekiti (FUOYE) Ta Dakatar Da Dalibai Biyu Kan Zargin Yada Bidiyon tsiraici Na Shugaban Daliban jami'ar.

Hukumar gudanarwar Jami’ar Tarayya da ke Oye-Ekiti (FUOYE) ta dakatar da dalibai biyu bisa zargin yada wani bidiyon tsiraici da ya shafi Shugaban Kungiyar Dalibai (SUG), James Iyanuoluwa Adio.

Jami’ar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Tajudeen Opoola, ya fitar ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, an zargi daliban biyu — Alao Iyanuoluwa Odunayo da Olawale Abiodun Samuel — da hada baki wajen cin zarafin Adio ta yanar gizo ta hanyar yada bayanansa na sirri bayan wata takaddama kan batun kudi.

Jami’ar ta ce ta yi Allah-wadai da lamarin, tana mai cewa irin wannan dabi’a na iya bata sunan jami’ar.

FUOYE ta kuma ce bincike kan lamarin yana ci gaba, sannan ta umurci daliban biyu da su dakatar da zuwa makaranta har sai an kammala bincike.

Wannan na zuwa ne bayan da aka dakatar da Shugaban SUG din a baya kan wasu zarge-zargen karbar kudade daga dalibai.

0 $type={blogger}: