Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai kan Lebanon, inda ta ce Amurka ce ke da alhakin kai tsaye kan halin da ake ciki.
Iran ta kuma yi gargadin cewa lamarin na iya haifar da mummunan tasiri ga zaman lafiya da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun ce gwamnatin Iran ta bayyana damuwarta ne bayan ci gaba da samun hare-hare tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon, duk da ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
A cewar rahoton Reuters, Iran ta ce duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiyar yankin zai iya jawo sakamako mai tsanani.

0 $type={blogger}:
Post a Comment