Jam’iyyar NDC Ta Tsayar da Ɗan Kwankwaso a Matsayin Dan Takarar Mataimakin Gwamna a jihar Kano.

Jam’iyyar NDC Ta Tsayar da Ɗan Kwankwaso a Matsayin Dan Takarar Mataimakin Gwamna a jihar Kano.

An nada Mustapha Kwankwaso, babban ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Kano.

An bayyana nadin ne a ranar Litinin ta bakin kakakin Kwankwaso, Saifullahi Hassan, a wata sanarwa ta gaggawa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan tsohon gwamnan da ke titin Miller Road a Kano.

Mustapha Kwankwaso ya taɓa rike mukamin Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano kafin ya yi murabus daga mukamin a watan Janairu.

Zaɓensa a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninsa da Aminu Abdulsalam, wanda shi ma ya taɓa kasancewa a Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano a ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Wannan sauyin siyasa ya biyo bayan sauya sheƙar Gwamna Yusuf, wanda aka zaɓe shi a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Sauya shekar ta haifar da rikice-rikicen siyasa a jihar, inda wasu jami’an gwamnati da abokan siyasa suka tsinci kansu cikin zaɓin ko su ci gaba da aiki a gwamnati ko su koma wajen Kwankwaso.

Ana sa ran wannan mataki na NDC zai taka muhimmiyar rawa a tseren zaɓen gwamnan Kano mai zuwa.

0 $type={blogger}: