‘Yan sanda sun ceto wata mata da aka daure da sarka sama da Sshekara daya a Abuja.

‘Yan sanda sun ceto wata mata da aka daure da sarka sama da Sshekara daya a Abuja.

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta ceto wata mata mai shekaru 36, Grace Aniekuoku, wadda ake zargin ɗan’uwanta, Chinedu Aniekuoku, ya daure da sarka tare da killace ta a wani ɗaki na tsawon shekara daya da watanni huɗu a Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan FCT, Ahmed Sanusi, ya bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa a ranar 12 ga Mayu dangane da halin da matar ke ciki.

Ya ce nan take aka tura jami’an bincike daga ofishin ’yan sanda na Katampe zuwa wurin da lamarin ya faru.

A cewarsa, da jami’an suka isa, wanda ake zargin ya nuna adawa tare da hana su shiga gidan da aka tsare ’yar uwarsa. Sai dai jami’an sun yi amfani da karfi wajen shiga ɗakin, inda suka tarar da matar a daure da sarka cikin matsanancin rashin lafiya da yunwa, tare da rayuwa cikin kazanta.

An kama wanda ake zargin nan take, yayin da aka ceto matar tare da kai ta asibiti domin samun kulawar likitoci, inda har yanzu take karbar magani.

Binciken farko ya nuna cewa an tafi da ɗan matar zuwa wani wuri da ba a sani ba kimanin shekaru biyu da suka gabata. ’Yan sanda sun ce daga baya wanda ake zargin ya killace ’yar uwarsa domin hana ta neman bayani kan inda aka kai ɗan na ta.

Rundunar ’yan sanda ta ce ana ci gaba da kokarin gano inda yaron yake da kuma ceto shi, yayin da bincike kan lamarin ke gudana.

A halin yanzu, wanda ake zargin na ci gaba da zama a hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

0 $type={blogger}: