Iran Ta Rufe Mashigar ruwan Hormuz Bayan Zargin Hare-Haren Isra’ila a Lebanon.

Iran Ta Rufe Mashigar ruwan Hormuz Bayan Zargin Hare-Haren Isra’ila a Lebanon.

Rundunar soji ta Iran ta bayyana cewa ta rufe mashigar Hormuz a matsayin martani ga hare-haren Isra’ila da aka kai a kudancin Lebanon.

Iran ta ce hare-haren sun saba yarjejeniyar da ta kulla da Amurka, inda ta bayyana matakin a matsayin martani kan abin da ta kira keta yarjejeniyar.

Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya, kuma rufe ta na iya shafar zirga-zirgar jiragen ruwa da kasuwar makamashi ta duniya.

Hukumomi na ci gaba da sa ido kan lamarin yayin da ake fargabar ƙarin tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

0 $type={blogger}: