Mutum ɗaya ya rasu bayan wasu jiragen ƙasa biyu masu ɗaukar kaya suka yi karo da juna a kan wata gada a birnin Munich na ƙasar Jamus da sanyin safiyar Asabar.
’Yan sanda na yankin sun ce hatsarin ya sa wasu kwantena biyu na jirgin sun fita daga kan layin dogon, inda suka faɗo daga gadar zuwa hanyar da ke ƙasa.
Har yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin, kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana.
An sanar da ma’aikatan agaji game da hatsarin da misalin ƙarfe 1:40 na dare a yankin Milbertshofen da ke arewacin birnin Munich.
Kuma an tura masu aikin ceto kusan 60 zuwa wurin.
Hukumomi na ci gaba da bincike kan yadda wannan hatsari mai muni ya faru.

0 $type={blogger}:
Post a Comment