Akalla gawarwakin 'yan cirani 15 ne aka tsinta, ciki har da wata yarinya, a bakin tekun Bahar Rum na gabashin Libya bayan wani jirgin ruwa da ake zargin yana ɗauke da mutane da dama 'yan cirani ya kife.
Majiyoyin tsaro da sojojin ruwa da jami’an lafiya sun ce jirgin yana ɗauke da kusan mutane 61, kamar yadda wasu 10 da suka tsira suka bayyana.
An tsinci gawarwakin ne a wurare daban-daban a bakin tekun Tobruk, wani gari da ke kusa da iyakar Masar. Jami’ai sun ce wasu daga cikin gawarwakin sun riga sun lalace sosai, kuma ana iya samun ƙarin gawarwakin.
Hotunan da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Tobruk ta wallafa sun nuna masu aikin ceto sanye da kayan kariya suna ɗaukar gawarwakin daga bakin duwatsu zuwa cikin fararen jakunkuna.
Tun bayan kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011, Libya ta zama hanyar wucewa ga ’yan cirani da ke tserewa yaƙe-yaƙe da talauci zuwa Turai ta hanyoyi masu haɗari na hamada da Bahar Rum.

0 $type={blogger}:
Post a Comment