Ƙungiyar Agaji ta Red Crescent ta Iran ta sanya hannu kan yarjejeniya da wani kamfanin jiragen sama na Rasha domin sayen jirage masu saukar angulu guda 20, domin ƙarfafa ayyukan ceto ta sama da jigilar kayan agaji a ƙasar.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Moscow tsakanin shugaban Red Crescent na Iran, Pirhossein Kolivand, da shugaban kamfanin Russian Helicopters, Nikolai Kolesov.
Kolivand ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wata muhimmiyar nasara a tarihin ƙungiyar agajin Iran, yana mai cewa sayen jiragen zai ƙara ƙarfin rundunar jiragen agaji ta ƙasar.
Ya ce an riga an kammala yarjejeniya ta ƙarshe kan jirage huɗu daga cikin 20, kuma ana sa ran isar da su kafin bikin sabuwar shekarar Iran a watan Maris na 2027.
A cewarsa, jiragen za su kasance da sabbin fasahohi ciki har da na’urorin hangen dare domin ba da damar gudanar da ayyukan ceto da dare. Haka kuma za a sanya musu kayan kashe gobara da na taimakon gaggawa na lafiya.
Sayen jiragen na daga cikin shirin Iran na ƙarfafa shirin tunkarar bala’o’i da inganta ayyukan agaji, musamman a yankunan da ke nesa ko masu fuskantar matsalolin gaggawa.
Iran da Rasha na ci gaba da ƙara haɗin gwiwa a fannoni daban-daban kamar makamashi da sufuri da tsaro.

0 $type={blogger}:
Post a Comment