Adadin mutanen da aka kashe a Gaza tun bayan “yarjejeniyar tsagaita bude Wuta” tsakanin Hamas da Isra’ila ya Wuce 1,000.


Fiye da Falasɗinawa 1,000 ne aka kashe a Gaza tun bayan yarjejeniyar “tsagaita wuta” da Amurka ta shiga tsakani Hamas da Isra’ila a watan Oktoba, yayin da matsalar jin ƙai a yankin ke ƙara taɓarɓarewa.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa hare-haren Isra’ila a sassan Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane 1,005 tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a watan Octoba.

Fikr Shalltoot, daraktar ƙungiyar Medical Aid for Palestinians a Gaza, ta ce: “Muna jimamin sabon mummunan tarihi da Gaza ta kai. Dubban mutane da aka gaya musu cewa matsala ta ƙare har yanzu suna binne ƙaunatattunsu.”

Tsagaita wutar ya dakatar da manyan hare-hare, amma ba a cimma yarjejeniya kan mataki na gaba ba, wanda ya haɗa da janye sojojin Isra’ila daga Gaza da kuma batun makaman Hamas.

Rahotanni sun ce tun watan Oktoba, Isra’ila ta ƙara faɗaɗa ikon da take da shi a Gaza, inda yanzu take iko da kusan kashi 64 cikin 100 na yankin Gaza.

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da harkokin jin ƙai (OCHA) ta ce wasu iyalai a gabashin Gaza City an tilasta musu barin gidajensu bayan da sojojin Isra’ila suka sanya alamun nuna faɗaɗa wani sabon layin soja.

An kuma yi tsammanin tsagaita wutar zai ba da damar sake gina Gaza da tsarin kiwon lafiyarta, amma OCHA ta ce asibitoci 20 ne kawai daga cikin 37 ke aiki a wani ɓangare, kuma babu wani asibiti da yake aiki gaba ɗaya.

Ƙungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa takaita shigar da kayan agaji na ci gaba da ƙara tsananta halin da ake ciki, musamman ƙarancin magunguna da kayan masarufi.

Tun bayan fara yaƙin a watan Oktoba, an kashe dubban Falasɗinawa, an lalata manyan sassan Gaza, kuma kusan mutane miliyan 1.9 sun rasa matsugunansu.

0 $type={blogger}: