Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta fara gasar Kofin Duniya na 2026 da gagarumar nasara bayan ta doke Croatia da ci 4-2, inda kyaftin ɗinta Harry Kane ya zura ƙwallaye biyu a ragar abokan hamayya a rabin lokaci.
Kane ne ya fara jefa ƙwallo bayan ya ci bugun fenariti da aka sake ba Ingila, bayan binciken VAR ya nuna cewa mai tsaron ragar Croatia, Dominik Livakovic, ya motsa daga layinsa kafin bugun farko.
Sai dai Croatia ta dawo wasan inda Martin Baturina da Petar Musa suka rama ƙwallaye biyu, lamarin da ya sa aka je hutun rabin lokaci 2-2 .
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Jude Bellingham ya sake bai wa Ingila jagoranci da ƙwallo ta uku, kafin ɗan wasan da ya shigo daga benci, Marcus Rashford, ya kammala nasarar da ƙwallo ta huɗu a ƙarshen wasan.
Wasan ya kasance maimaituwar karawar da aka yi a wasan kusa da ƙarshe na Kofin Duniya na 2018, inda Croatia ta doke Ingila, amma wannan karon tawagar kocin Thomas Tuchel ta samu nasara.
Ƙwallaye biyun Kane sun kai adadin ƙwallayen da ya ci a gasar Kofin Duniya zuwa 10, inda ya yi daidai da tsohon ɗan wasan Ingila Gary Lineker a matsayin wanda ya fi cin ƙwallaye a gasar ta duniya a tarihin Ingila.
Ingila, wadda ke neman lashe babban kofi na farko tun shekarar 1966, ta fara gasar da kwarin gwiwa bayan wannan gagarumar nasara.

0 $type={blogger}:
Post a Comment