Darajar Naira Ya Faɗi Zuwa N1,405 Kan Dala Daya A Kasuwar Bayan Fage.

Darajar Naira Ya Faɗi Zuwa N1,405 Kan Dala Daya A Kasuwar Bayan Fage.

Darajar kuɗin Najeriya, Naira, ya sake yin ƙasa, inda aka fara sayar da dala daya akan N1,405 a kasuwar bayan fage, idan aka kwatanta da N1,389 da aka sayar a ranar Talata.

Haka kuma, nairar ta yi rauni a kasuwar canjin kuɗi ta Najeriya (NFEM), inda farashin dala ya tashi zuwa N1,361.5 daga N1,356.5 kan dala, wanda ke nuna raguwar darajar naira da N5.

Bambancin farashin dala tsakanin kasuwar bayan fage da kasuwar gwamnati ya ragu zuwa N43.5 kan dala, daga N32.5 da aka samu a baya.

A halin yanzu, hada-hadar canjin kuɗi a kasuwar NFEM ta ragu sosai, inda cinikin ya sauka da kashi 56.8 cikin 100, daga N125.7 miliyan zuwa N54.3 miliyan a ranar Laraba.

0 $type={blogger}: