Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB Ta Dakatar da Shirin karatun Digiri na Hadaka a Kwalejojin Ilimi.

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB Ta Dakatar da Shirin karatun Digiri na Hadaka a Kwalejojin Ilimi.

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya (JAMB) ta dakatar da karbar sabbin dalibai a shirin karatun digiri na hadaka da ake gudanarwa a Kwalejojin Ilimi.

Wannan sabon matakin ya kawo babban sauyi a tsarin koyar da malamai a Najeriya, inda JAMB ta ce shirin Takardar Shaidar Ilimi ta Najeriya (NCE) ne zai zama babbar hanyar shiga Kwalejojin Ilimi daga zangon karatu na shekaran 2026/2027.

A cikin sabbin ka’idojin rajistar NCE/ND Agric da hukumar ta fitar, JAMB ta bayyana cewa ba za a sake karbar dalibai zuwa shirin karatun digiri na hadaka a kowanne Kwalejin Ilimi ba daga zangon shekaran 2026/2027.

Hukumar ta kuma haramta shiga kai tsaye zuwa matakin aji na 100 da 200 a Kwalejojin Ilimi, inda ta ce duk sabbin dalibai dole ne su fara ta hanyar shirin NCE.

JAMB ta ce wannan matakin ya kawo karshen tsarin da aka shafe shekaru ana yi, inda Kwalejojin Ilimi ke bayar da digiri ta hanyar hadin gwiwa da jami’o’i.

Ana sa ran wannan sauyi zai shafi dubban dalibai da suka nemi shiga shirin karatun digiri ta Kwalejojin Ilimi a shekarar karatu ta 2026.

Domin rage matsalar ga wadanda abin ya shafa, JAMB ta samar da hanyoyi kamar sauya makaranta da komawa jami’ar da ke da alaka da shirin, ko kuma komawa shirin matakin NCE.

Hukumar ta ba wa masu son sauya makaranta wa’adin zuwa ranar 22 ga Yuni domin kammala sauyin.

0 $type={blogger}: