Dubun Dubatan Masu Zanga-zanga ne Su ka fito kan tituna a ƙasar Albania domin nuna rashin amincewarsu da Shirin Gina Katafaren Gidan Hutu Mai Alaƙa da iyalin Donald Trump.

Dubun Dubatan Masu Zanga-zanga ne Su ka fito kan tituna a ƙasar Albania domin nuna rashin amincewarsu da Shirin Gina Katafaren Gidan Hutu Mai Alaƙa da iyalin Donald Trump.

Dubun Dubatan masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tirana, babban birnin ƙasar Albania, domin nuna adawa da wani shirin gina katafaren wurin yawon buɗe ido da ake danganta shi da iyalan Shugaban Amurka Donald Trump.

Shirin gina otal ɗin, wanda ake danganta shi da Jared Kushner da Ivanka Trump, ya jawo fushi daga ƙungiyoyin kare muhalli da wasu ’yan ƙasa, waɗanda ke cewa aikin na iya yin illa ga wani yanki da aka ware domin kare muhalli.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki suna ɗauke da tutocin Albania da Amurka, suna rera taken “Ba a sayar da Albania ba”, tare da neman gwamnati ta bayyana cikakken bayani kan shirin.

Ana shirin gina wurin hutun ne kusa da yankin Vjosa-Narta mai kariya, wanda ya shahara da namun daji da tsuntsayen ƙaura ciki har da flamingo. Masu adawa da aikin na ganin zai iya lalata muhalli da halittu.

Masu zanga-zangar sun kuma zargi Firayim Minista Edi Rama da amincewa da yarjejeniyoyin da ba a bayyana su ba, tare da neman ya yi murabus.

Sai dai Rama ya ƙi amincewa da kiran murabus ɗin, yana cewa hayaniyar ta fi karkata ne kan alaƙar shirin da sunan Trump da Kushner fiye da ainihin aikin.

Zanga-zangar ta ci gaba tsawon makonni, inda wasu ’yan asalin Albania da ke ƙasashen waje suka koma gida domin shiga cikin jerin masu nuna adawar.

0 $type={blogger}: