Donald Trump Ya Ce Starmer Zai Yi Murabus A Matsayin Fira Ministan Birtaniya.

Donald Trump Ya Ce Starmer Zai Yi Murabus A Matsayin Fira Ministan Birtaniya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, zai sauka daga mukaminsa, yana mai cewa hakan ya samo asali ne daga gazawa a bangaren shige da fice da manufofin makamashi.

Trump ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadi ta shafinsa na Truth Social, yayin da gwamnatin Starmer ke fuskantar matsin lamba daga masu suka a cikin kasar.

“Keir Starmer zai yi murabus daga matsayin Fira Ministan Birtaniya,” in ji Trump, inda ya zargi Starmer da rashin samun nasara kan batutuwan shige da fice da makamashi.

Sai dai shugaban Amurkan bai gabatar da wata hujja ba ko bayyana inda ya samo wannan ikirarin.

Starmer, wanda shi ne shugaban jam’iyyar Labour, ya zama Firayim Minista bayan jam’iyyarsa ta lashe babban zaben Birtaniya. Gwamnatinsa na fuskantar suka kan batutuwa da suka hada da bakin haure, manufofin makamashi da matsalolin tattalin arziki.

0 $type={blogger}: