Shahararren ɗan bindigar nan, Bello Turji, ya bayyana a wani sabon bidiyo yana cewa mutanensa ne suka kai harin da ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji a Jihar Sakkwato.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan da dakarun soji suka nufi garin Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa domin kai ɗauki sakamakon wani harin ’yan bindiga da aka kai da sanyin safiyar Asabar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne tsakanin tsakar dare zuwa kusan ƙarfe 3 na safe, inda suka yi ta harbe-harbe tare da tayar da hankalin jama’a.
Yayin da sojojin ke kan hanyar zuwa wajen, wata na’ura mai fashewa da aka dasa a hanya ta tashi, inda ta lalata motarsu a hanyar Isa zuwa Bargaja.
Rahotanni sun ce akalla sojoji biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu suka samu raunuka.
A cikin bidiyon da ya fitar, Turji ya ce yana murnar abin da ya kira nasara kan jami’an tsaro, tare da ikirarin cewa mutanensa sun kwato wasu dabbobi daga hannun jami’an.
Sai dai hukumomin tsaro ba su tabbatar da ikirarin ba, kuma ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.
Wannan lamari ya ƙara jawo damuwa a yankunan Sakkwato da Zamfara, inda ake ci gaba da fama da matsalar hare-haren ’yan bindiga.
Source Dailytrust

0 $type={blogger}:
Post a Comment