Australia Ta Tsawaita Rangwamen Harajin Man Fetur Domin Rage Matsin Rayuwa ga 'Yan ƙasar.

Australia Ta Tsawaita Rangwamen Harajin Man Fetur Domin Rage Matsin Rayuwa ga 'Yan ƙasar.

Gwamnatin Australia ta sanar da tsawaita rangwamen harajin man fetur na tsawon wata guda domin rage tasirin hauhawar farashin mai da matsin tattalin arziki ga jama’an ƙasar.

Fira Ministan ƙasar, Anthony Albanese ya ce wannan matakin zai sa farashin man fetur da dizal su kasance ƙasa da na yau da kullum da cents 16 a kowace lita a cikin watan Yuli, lamarin da zai ceci masu amfani da mota kusan dala 11 na Australia a kowace tanki.

Albanese ya bayyana cewa wannan ƙarin tallafi na ɗan lokaci zai taimaka wajen rage nauyin hauhawar farashin mai tare da taimaka wa ‘yan ƙasa wajen fuskantar tsadar rayuwa.

Gwamnatin ta riga ta rage harajin man fetur tare da dakatar da wani ƙarin kuɗin amfani da hanya na tsawon watanni uku, bayan da farashin mai ya ƙaru sakamakon rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya.

Australia, wadda ke shigo da mafi yawan man fetur daga ƙasashen waje, ta fuskanci matsalolin samar da mai da hauhawar farashin makamashi sakamakon tashe-tashen hankula da suka shafi Iran.

Fira Ministan ya ce iyalai na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki, kuma tasirin rikicin ƙasashen duniya na iya ci gaba da shafar tattalin arziki na wani lokaci mai tsawo.

Wannan matakin ya biyo bayan shawarar gwamnati na ci gaba da fitar da fetur da dizal daga ma’ajiyar ƙasar har zuwa watan Satumba domin tabbatar da wadatar mai.

Gwamnati ta ce waɗannan matakai na da nufin tallafa wa jama’a yayin da kasuwar makamashi ta duniya ke fuskantar rashin tabbas.

0 $type={blogger}: