Hukumar Lafiya ta ƙasar Faransa Ta Ce Kimanin Mutane 1,000 ne Suka Mutu Sakamakon Zafin Rana Mai Tsanani.

Hukumar Lafiya ta ƙasar Faransa Ta Ce Kimanin Mutane 1,000 ne Suka Mutu Sakamakon Zafin Rana Mai Tsanani.

Jami’an lafiya a Faransa sun bayyana cewa mutane kusan 1,000 ne suka mutu sakamakon matsanancin zafin rana da ya mamaye yankunan yammacin Turai na tsawon kwanaki.

Hukumar Lafiyar Jama’a ta Faransa  ta ce tun daga ranar 24 ga watan Yuni, an samu kusan mutuwar karin mutane 1,000 idan aka kwatanta da adadin mutuwar da aka samu a watannin baya.

Hukumar ta bayyana cewa yankunan da aka sanya wa matakin gargadin zafi mai tsanani sun fi fuskantar matsalar, inda kashi 85 cikin 100 na wadanda suka mutu suka kasance mutane masu shekaru 65 zuwa sama.

Ta ce mafi yawan karuwar mace-macen an fi ganinsu ne a tsakanin mutanen da suka mutu a gidajensu, musamman a yankin Île-de-France, wanda ya hada da birnin Paris da kewayensa.

Hukumar ta yi gargadin cewa alkaluman da aka fitar na wucin gadi ne, kuma akwai yiwuwar adadin mutuwar ya fi haka yawa.

Zafin rana ya tilasta wasu sassan Faransa fuskantar yanayin da ya haura digiri 40 na ma’aunin Celsius, kafin yanayin ya fara sauki a ranar Lahadi.

Mahukuntan lafiya sun bukaci jama’a da su rika duba lafiyar tsofaffi da mutanen da ke zaune su kadai domin kare su daga illar matsanancin zafi.

0 $type={blogger}: