Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da iyalan Ummulkhairi Aliyu, matar da wasu fusatattun jama’a suka kashe a Maraban Jos, ƙaramar hukumar Igabi.
Gwamnan ya ce gwamnati za ta tallafa wa mijin marigayiyar da ’ya’yanta huɗu, ciki har da daukar nauyin karatunsu.
Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamaciyar, kusan makonni biyu bayan faruwar lamarin.
An ruwaito cewa Ummulkhairi, wadda malamar addinin Musulunci ce, an yi mata duka har ta mutu a ranar 14 ga watan Yuni bayan zargin cewa ta yi yunkurin sace yara. Daga bisani wasu suka kona gawarta kafin jami’an tsaro su dawo da zaman lafiya a yankin.
Gwamnan ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai bayyana shi a matsayin abin kunya da rashin tausayi, tare da tabbatar wa iyalan cewa za a yi musu adalci.
Ya ce hukumomin tsaro na aiki domin tabbatar da an kama duk wadanda ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Gwamnan ya bayyana cewa tuni aka gurfanar da mutane 41 bisa zargin kisan kai, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu da ake zargi.
Uba Sani ya jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a kisan zai fuskanci hukunci bisa doka, yana mai cewa babu wanda ke da ikon daukar doka a hannunsa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment