Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar katafaren kamfanin mai na Saudi Arabiya, Saudi Aramco, ya yi hatsari a ranar Lahadi a yankin Ras Tanura da ke gabashin ƙasar, inda ya yi sanadin mutuwar ’yan ƙasar Saudiyya 14, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta gwamnati ta ruwaito.
Mahukunta sun bayyana cewa har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba, kuma an fara gudanar da bincike tare da hukumomin da abin ya shafa domin gano yadda lamarin ya faru.
Hatsarin ya faru ne kusa da wuraren hakar da fitar da man Ras Tanura, wanda yake ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin fitar da man fetur na Saudiyya a gabar Tekun Gulf. Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kamfanin Saudi Aramco ya sake dawo da ayyukan lodin ɗanyen mai a tashar bayan dakatarwar da aka yi na kusan watanni huɗu.
Saudiyya, wadda ita ce ƙasa mafi girma wajen fitar da mai a duniya, ta ƙara ƙoƙarin jigilar man fetur zuwa kasuwannin duniya yayin da ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya suka ƙara samarwa da fitar da mai a yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya domin cimma yarjejeniya ta wucin gadi don kawo ƙarshen rikicin tsakanin Amurka da Iran.

0 $type={blogger}:
Post a Comment