Aƙalla Mutane 8 ne Suka Rasa rayukansu, yayin da 17 Suka Jikkata a Hadarin Mota a jihar Katsina.

Aƙalla Mutane 8 ne Suka Rasa rayukansu, yayin da 17 Suka Jikkata a Hadarin Mota a jihar Katsina.

Akalla mutane takwas ne suka mutu, yayin da wasu 17 suka samu raunuka daban-daban sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Funtua zuwa Katsina, a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), reshen Katsina, ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana, ranar Lahadi a yankin Layin Kukah da ke kan hanyar Funtua zuwa Katsina.

Hatsarin ya haɗa da wata motar haya kirar Toyota Hiace mai lamba 14B 92 TR da kuma babur mai kafa uku (Bajaj) wanda ba shi da lamba.

FRSC ta ce mutane 25 ne abin ya shafa, inda 17 suka samu raunuka, yayin da 8 suka rasa rayukansu.

Binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa wucewa ba tare da tsari ba (wrongful overtaking) ne ya haddasa hatsarin.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na FRSC, DRC Shamsudeen Babajo, ya ce tawagar ceto ta isa wurin da lamarin ya faru bayan mintuna 30 da samun rahoton hatsarin.

Ya ƙara da cewa an yi aikin ceto tare da haɗin gwiwar Community Watch Corps, inda aka kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Ƙwararru na Bakori domin samun kulawa, yayin da aka kai gawarwakin zuwa Babban Asibitin Funtua.

FRSC ta yi kira ga direbobi da su guji wucewar da ba ta da tsaro tare da bin dokokin hanya domin rage yawan haɗurran ababen hawa.

0 $type={blogger}: