Rundunar ’yan sandan jihar Imo ta ce ta ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi yayin wani samame na musamman da aka gudanar domin fatattakar masu aikata laifuka a wasu sassan karamar hukumar Owerri ta yamma.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Imo, CP Audu Bosso, ne ya jagoranci aikin tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na sa-kai, inda suka kai farmaki a yankunan dajin Nekede da Ihiagwa da Agbala.
Mai magana da yawun rundunar, Henry Okoye, ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bisa umarnin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, domin lalata maboyar masu laifi tare da tabbatar da tsaro a jihar.
A yayin aikin, jami’an tsaron sun gano tare da ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi mai suna Chinonaobi Uchegbulam daga Ubaha Orodo, wanda aka same shi a wani maboyar daji.
Rundunar ta ce an garzaya da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa, kuma yana samun sauki.
CP Bosso ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin saboda jajircewa da kwarewa, yana mai cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da hare-haren sirri domin yaki da masu aikata laifuka.
Ya kuma bukaci al’umma su kasance masu lura da kai tare da sanar da jami’an tsaro duk wani abu da ake zargi, domin taimakawa wajen dakile garkuwa da mutane da sauran laifuka.

0 $type={blogger}:
Post a Comment