Hatsarin Jirgin Helikwafta na Sojin Pakistan Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Duk Mutanen da Ke Cikin jirgin.

Hatsarin Jirgin Helikwafta na Sojin Pakistan Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Duk Mutanen da Ke Cikin jirgin.

Wani jirgin helikwafta na sojin Pakistan ya yi hatsari a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan, kusa da birnin Muzaffarabad, inda hukumomi suka tabbatar cewa duk mutanen da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu.

Sojojin Pakistan sun bayyana cewa jirgin samfurin Mi-17 na rundunar jiragen sama ta sojin ƙasar ya fadi ne jim kaɗan bayan tashinsa saboda matsalar fasaha.

Rahotanni sun ce babu wanda ya tsira daga cikin jirgin, duk da cewa ba a bayyana adadin mutanen da ke ciki ba a hukumance.

Lamarin ya faru ne a yankin Kashmir, wanda ke daga cikin wurare masu matuƙar rikici tsakanin Pakistan da India, inda kasashen biyu ke da’awar mallakarsa gaba ɗaya amma kowanne ke rike da wani bangare.

A ‘yan kwanakin nan an ƙara tsaurara tsaro a Muzaffarabad sakamakon zanga-zangar da wata ƙungiya ta shirya, wadda daga baya hukumomi suka hana bisa dokokin yaƙi da ta’addanci.

Sojojin sun ce za a gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin faruwar hatsarin.

0 $type={blogger}: