Wasu 'yan bindiga sun kai hari wata makarantar sakandare da ke jihar Kogi a yau Laraba, inda suka kashe mutum uku ciki har da mataimakin shugaban makarantar, tare da yin garkuwa da wasu ɗalibai, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Lamarin ya faru ne a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Iluke Bunu da ke ƙaramar hukumar Kabba-Bunu yayin da ɗalibai ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta Yammacin Afirka (WASSCE).
Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga makarantar ne da misalin ƙarfe 9:45 na safe, inda suka kai farmaki cibiyoyin jarabawa wanda ɗalibai daga al’ummomi daban-daban suka taru domin rubuta jarabawar.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai Mataimakin Shugaban Makarantar, Mista Gani Anifowose, da Mista Sunday Jacob Alhassan mai shekaru 70, da kuma yaro ɗan shekara shida mai suna Sunday Ayele.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa aƙalla ɗalibai uku da wasu mazauna garin an yi garkuwa da su yayin harin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu, Zacchaeus Dare Michael, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici da rashin tausayi da kuma wanda ba za a amince da shi ba.
Ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da tabbatar da cewa jami'an tsaro na aiki domin cafke masu laifin.
Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kogi ta ce maharan masu ɗauke da muggan makamai, waɗanda suka zo kan kusan babura 40, sun mamaye yankin da nufin yin garkuwa da ɗalibai da mazauna yankin.
Kakakin rundunar, ASP Saliu Oyiza, ya ce jami'an tsaro da suka haɗa da 'yan sanda da sojoji da jami'an rundunar MOPOL da masu sa kai sun gaggauta mayar da martani tare da fafatawa da maharan.
A cewarsa, jami'an tsaron sun tilasta wa maharan tserewa zuwa cikin daji bayan musayar wuta mai zafi. An kashe ɗaya daga cikin maharan yayin fafatawar, yayin da wani jami'in tsaro ya samu raunin harbin bindiga kuma yake karɓar magani.
Sai dai rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa bincike na ci gaba, kuma har yanzu ba a tabbatar da cewa an yi garkuwa da ɗalibai masu yawa ba.
A halin yanzu, jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da samame da bincike domin cafke maharan da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment