Wani fashewa ya faru a cibiyar iskar gas ta Barzan da ke yankin masana’antu na Ras Laffan a ƙasar Qatar, inda mutane 54 suka jikkata, yayin da ake neman wasu mutane 18 da suka ɓace.
Lamarin ya faru ne a daren Lahadi 21 ga Yuni, lokacin da ake ƙoƙarin sake kunna ayyukan kamfanin gas ɗin, wanda ke samar da iskar gas ga masana’antu da bangaren samar da wutar lantarki na ƙasar.
Jami’an tsaro da ma’aikatan ceto daga hukumar kashe gobara ta Qatar da ƙungiyar binciken ceto ta ƙasa da ƙasa sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto.
Mahukunta sun ce an shawo kan gobarar da ta tashi bayan fashewar.
Hukumomi sun bayyana cewa ana zargin matsalar fasaha ce ta haddasa lamarin yayin gudanar da aiki, kuma babu wata matsalar zubar gas da ke barazana ga jama’a.
Kamfanin Barzan na da muhimmiyar rawa a tsarin makamashin Qatar, domin yana samar da gas da ake amfani da shi wajen samar da wutar lantarki da tace ruwa da kuma masana’antun cikin gida.
Kamfanin makamashin QatarEnergy bai bayyana cikakken adadin barnar da aka yi ba ko lokacin da za a dawo da ayyukan kamfanin yadda suke.
A halin yanzu, jami’an ceto na ci gaba da neman mutanen da suka ɓace, yayin da ake gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin fashewar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment