Zazzabin Lassa Ya Kashe Mutane 214 a Najeriya – NCDC

Zazzabin Lassa Ya Kashe Mutane 214 a Najeriya – NCDC

Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa annobar zazzabin Lassa ta kashe mutane 214 a Najeriya, yayin da adadin mace-macen ya karu zuwa kashi 25 cikin 100.

NCDC ta bayyana hakan ne a rahoton halin da ake ciki na zazzabin Lassa na mako na 23, wanda ya shafi daga 1 zuwa 7 ga Yunin 2026.

Hukumar ta ce yawan mace-macen ya karu sosai idan aka kwatanta da kashi 18.9 cikin 100 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2025.

Yadda Zazzabin Lassa Ya Bazama Zuwa Jihohi 23

NCDC ta ce adadin masu kamuwa da cutar da kuma waɗanda ake zargi da kamuwa da ita ya ƙaru, inda aka samu sabbin rahotanni daga jihohin Edo, Ondo, Bauchi da Ebonyi.

Tun daga watan Janairu 2026, cutar ta bazu zuwa jihohi 23 da ƙananan hukumomi 109 a ƙasar.

Jihohi biyar ne suka fi yawan masu kamuwa da cutar, inda suke da kusan kashi 84 cikin 100 na dukkan waɗanda aka tabbatar:

Ondo – kashi 28%

Bauchi – kashi 25%

Taraba – kashi 15%

Edo – kashi 10%

Benue – kashi 6%


Sauran kaso na cutar yana rarrabuwa a wasu jihohi 18.

Matasa Ne Suka Fi Shafa

Hukumar ta ce matasa ne suka fi kamuwa da cutar, musamman masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30.

An samu masu fama da cutar daga jariri mai shekara ɗaya zuwa tsoho mai shekara 93, yayin da matsakaicin shekarun masu kamuwa da ita ya kai kusan 30.

NCDC Na Ci Gaba Da Yaki Da Annobar

NCDC ta ce tsarin gaggawa na ƙasa domin dakile zazzabin Lassa yana ci gaba da aiki domin tallafa wa jihohi da ƙananan hukumomi wajen magance cutar.

Duk da cewa ba a samu sabon kamuwa da cutar a tsakanin ma’aikatan lafiya a wannan makon ba, hukumar ta yi gargadin cewa yawan mace-mace da bazuwar cutar na nuna cewa cutar tana ci gaba da yaɗuwa.

Ana ci gaba da sa ido, ba da magani, da kuma shirye-shiryen dakile cutar a jihohin da abin ya shafa.

0 $type={blogger}: