Fada Ya Barke a Majalisar Dokokin ƙasar Jojiya Yayin Zaman Ƙarshe na lokacin Bazara.

Fada Ya Barke a Majalisar Dokokin ƙasar Jojiya Yayin Zaman Ƙarshe na lokacin Bazara.

Wani rikici da aka ba hammata iska ya barke a cikin Majalisar Dokokin ƙasar Jojiya a ranar 26 ga watan Yuni, yayin da ‘yan majalisa daga jam’iyyar gwamnati ta Georgian Dream da ‘yan adawa na jam’iyyar For Georgia suka yi arangama.

Lamarin ya faru ne a lokacin zaman tambaya da amsa bayan Fira Minista Irakli Kobakhidze ya gabatar da rahoton aikinsa na shekara.

An ce rikicin ya fara ne bayan ɗan majalisar adawa Giorgi Sharashidze ya soki Kobakhidze kan rawar da ya taka yayin ziyarar Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev zuwa Jojiya.

Sharashidze ya yi ikirarin cewa hotunan ganawar Aliyev da wanda ya kafa jam’iyyar Georgian Dream, Bidzina Ivanishvili, sun nuna cewa Kobakhidze ba shi da cikakken iko a cikin jam’iyyar.

Maganganun nasa sun fusata wasu ‘yan majalisar gwamnati, lamarin da ya haifar da hayaniya kafin daga bisani aka fara duka.

Bidiyon da aka fitar ya nuna yadda wasu ‘yan majalisa suka yi musayar kalamai masu zafi sannan rikicin ya rikide zuwa dambe da ya shafi maza da mata.

Jami’an tsaron majalisar sun shiga tsakani tare da fitar da wasu ‘yan adawa daga zauren yayin da rikicin ke ci gaba.

An gano wasu ‘yan majalisar Georgian Dream da suka shiga rikicin ciki har da Lasha Talakhadze, zakaran gasar ɗaga nauyi na Olympic sau uku, da Archil Gorduladze, shugaban kwamitin shari’a na majalisar.

Daga bisani an kira jami’an agajin gaggawa zuwa ginin majalisar bayan faruwar lamarin.

A lokacin an dakatar da watsa zaman majalisar na ɗan lokaci yayin da jami’ai ke kokarin shawo kan rikicin.

0 $type={blogger}: