An kama manyan kwamandojin Boko Haram Da ISWAP su bakwai a filin jirgin katsina bayan dawowarsu daga Makka.

An kama manyan kwamandojin Boko Haram Da ISWAP su bakwai a filin jirgin katsina bayan dawowarsu daga Makka.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana kama wasu mutane bakwai da ake zargi da kasancewa manyan kwamandojin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a Filin Jirgin Sama na Katsina, bayan sun dawo daga aikin Hajji a Makka, ƙasar Saudiyya.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce an samu nasarar kama su ne sakamakon haɗa tsarin bayanan tantance ‘yan ƙasa na Najeriya da na hukumomin tsaro, ciki har da Hukumar Kula da Shige da Fice da kuma wasu hanyoyin tsaro na ƙasa da ƙasa.

Ya bayyana cewa an gano waɗanda ake zargin ne lokacin da suka sauka a Najeriya ta hanyar tsarin tantance bayanai, sannan aka miƙa su ga Hukumar SSS (DSS) domin gudanar da bincike.

Tunji-Ojo ya ce a baya Najeriya na da tsarin bayanai da ba su haɗu da juna, amma gyare-gyaren da aka yi yanzu sun haɗa bayanan hukumomi daban-daban domin ƙarfafa tsaro.

Ya ce haɗa bayanan Hukumar NIMC da na Shige da Fice tare da tsarin tsaro na Interpol ya taimaka wajen gano waɗannan mutane da ake nema.

Ministan ya bayyana wannan a matsayin babbar nasara a yaƙin da Najeriya ke yi da ta’addanci da satar bayanai da laifukan kuɗi da sauran laifukan da suka shafi ƙasashe daban-daban.

Ya ƙara da cewa sabon tsarin ya ƙarfafa tsaron iyakokin ƙasa da tattara bayanan sirri, tare da inganta tsarin bayar da fasfo ta hanyar tabbatar da sahihancin bayanan mutum.

0 $type={blogger}: