Ƙasar Bosnia da Herzegovina ta samu damar shiga zagayen fitar da gwani na gasar cin kofin duniya (World Cup) a karon farko a tarihinta, bayan da ta doke Qatar da ci 3-1 a wasan karshe na rukuni na biyu.
Nasarar ta kai Bosnia maki huɗu, sannan FIFA ta tabbatar da cewa ƙasar ta tsallake zuwa zagayen ‘yan wasa 32 a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi ƙwazo cikin waɗanda suka kare a matsayi na uku.
A gefe guda, Qatar ta fice daga gasar tun daga matakin rukuni, kamar yadda ta faru a gasar 2022. Sai dai wannan karon ta samu maki ɗaya, bayan da a baya ba ta samu ko maki ɗaya ba a gasar da ta shirya.
Dan wasan Bosnia mai shekaru 18, Kerim Alajbegovic, ne ya fara jefa ƙwallo mai kyau, inda ya zama ɗan wasan Bosnia mafi ƙanƙanta da ya taɓa zura ƙwallo a gasar cin kofin duniya. Daga baya mai tsaron ragar Qatar, Mahmoud Abunada, ya ci ƙwallon kansa, abin da ya bai wa Bosnia damar tafiya da ci 2-0.
Qatar ta dawo wasan ne kafin hutun rabin lokaci, bayan tsohon ɗan wasanta Hassan Al-Haydos ya rage tazarar zuwa 2-1.
Sai dai Bosnia ta tabbatar da nasarar a minti na 80, bayan Ermin Mahmic ya zura ƙwallo ta uku, wanda ya ba ƙasar damar samun wannan gagarumar nasara.
Wannan nasara ta zama tarihi ga Bosnia, yayin da Qatar ta kammala gasarta cikin rashin nasara duk da cewa ta nuna ci gaba fiye da wasanninta na gasar 2022.

0 $type={blogger}:
Post a Comment