Ƙasar Iran ta ce dole ne a shigar da batun Lebanon cikin yarjejeniyar Ƙarshe na kawo ƙarshen yaƙi da Kasar Amurka.

Ƙasar Iran ta ce dole ne a shigar da batun Lebanon cikin yarjejeniyar Ƙarshe na kawo ƙarshen yaƙi da Kasar Amurka.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce duk wani sabon hari da Isra’ila za ta kai wa Lebanon ko kuma ci gaba da mamaye wasu yankuna a ƙasar zai zama karya yarjejeniyar fahimtar juna da ake shirin sanyawa hannu tsakanin Iran da Amurka.

A yayin da yake magana da jami’an diflomasiyya a Tehran ranar Talata, Araghchi ya ce babban ginshiƙin yarjejeniyar shi ne a kawo ƙarshen yaƙin nan take kuma na dindindin a dukkanin ɓangarorin da rikicin ya shafa, ciki har da Lebanon.

Ya jaddada cewa kawo ƙarshen hare-hare kan Lebanon wani muhimmin ɓangare ne na duk wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai cewa ba za a samu zaman lafiya a yankin ba idan ba a aiwatar da yarjejeniyar gaba ɗaya ba.

Ministan ya ce rikicin da ya ƙara tsananta tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila ya haɗu da abubuwan da ke faruwa a Lebanon, don haka warware rikicin gaba ɗaya ya danganta da kawo ƙarshen faɗace-faɗacen.

Araghchi ya kuma yi kira da a janye sojojin Isra’ila daga yankunan da suka mamaye a lokacin rikicin, yana mai cewa ba za a ce an kawo ƙarshen yaƙin ba har sai an kammala janyewar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa an kammala daftarin yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, kuma za a sanya hannu a hukumance a Switzerland ranar Juma’a.

Ya ce matakin farko na tattaunawar ya mayar da hankali ne kan kawo ƙarshen yaƙin da sake buɗe mashigar ruwan Hormuz, da batutuwan da suka shafi takunkumi da kadarorin Iran da aka rike.

Araghchi ya ƙara da cewa za a ci gaba da tattaunawar neman cikakkiyar yarjejeniya na tsawon kwanaki 60, inda za a tattauna batutuwan nukiliya da cire takunkumi.

Ya kuma yaba wa Pakistan kan rawar da ta taka wajen taimaka wa tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.

0 $type={blogger}: