An yi jana’izar matashin dan kasuwar kayan kwalliya, Isma’il Makaye, wanda ya rasu a gidan budurwarsa, fitacciyar mai rawar solo kuma ‘yar TikTok a Kano, Fati Cele.
Rahotanni daga makusantansa sun bayyana cewa, da safiyar Juma’a ne Fati Cele ta fito daga cikin gidanta tana neman agaji, inda bayan shiga gidan aka tarar da Makaye ya rasu tare da wasu alamomin rauni da jini a jikinsa.
Wata majiya ta ce ‘yan sanda daga ofishin Dorayi Babba sun tsare Fati Cele domin gudanar da bincike kan lamarin.
Abokan marigayin sun bayyana cewa, a baya an samu rashin jituwa tsakaninsa da Fati Cele har suka rabu, kafin daga baya su sake sulhu.
Fati Cele, wadda ‘yar asalin jihar Borno ce, tana zaune a Danbare cikin ƙaramar hukumar Kumbotso ta Kano, kuma tana yin rawar solo a wani gidan gala da ke yankin Sabon Gari.
An kai gawar Makaye asibiti domin tabbatar da rasuwarsa kafin daga bisani aka yi jana’izarsa a Unguwa Uku Yan Awaki bisa tsarin addinin Musulunci.
Tuni abokai da masoyansa suka bayyana alhini a kafafen sada zumunta, musamman TikTok, tare da yin kira ga hukumomi su gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

0 $type={blogger}:
Post a Comment