Mai daukar hoto na Al Jazeera Mubasher ya rasu a harin Isra’ila a Gaza.

Mai daukar hoto na Al Jazeera Mubasher ya rasu a harin Isra’ila a Gaza.

An kashe mai daukar hoton tashar Al Jazeera Mubasher, Ahmed Washah, a wani harin sama da Isra’ila ta kai kan wani gida mai jama’a a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij, da ke tsakiyar yankin Gaza.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne yayin da ake ci gaba da ruwan bama-bamai a yankin, inda aka samu asarar rayuka.

Rasuwar Ahmed Washah ta janyo alhini, yayin da ake ci gaba da bayyana damuwa kan tsaron ma’aikatan kafafen yada labarai a yankin Gaza.

0 $type={blogger}: