Akalla wasu da ake zargin 'yan bindiga mutun shida ne suka mutu bayan da jami'an tsaro suka yi nasarar dakile wani hari da suka kai Kanoma da ƙauyen Gidan Daji da ke Gundumar Kanoma a Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Mai magana da yawun Rundunar 'Yan Sandan Jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Talata lokacin da ɗimbin 'yan bindiga dauke da manyan makamai suka mamaye yankunan.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun zo da manyan makamai na zamani da suka haɗa da roka masu linzami (RPG) da bindigogin GPMG da kuma bindigogin AK-47.
Bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin, jami'an tsaro da suka haɗa da rundunar 'yan sanda ta musamman daga Sashen Maru da sojojin da ke aiki ƙarƙashin Operation Fansar Yamma da jami'an Violence Crime Response Unit, da kuma masu sa-kai na yankin, sun garzaya wurin domin kai ɗauki.
Jami'an tsaron sun yi artabu mai tsanani da maharan, lamarin da ya tilasta musu janyewa tare da hana harin yin nasara.
A yayin fafatawar, an kashe 'yan bindiga shida da ke hawa babura guda biyu.
Yazid Abubakar ya ce wasu daga cikin maharan sun tsere zuwa cikin dazukan da ke kusa da wurin tare da raunukan harbin bindiga, yayin da ba a samu asarar rai ko rauni ba daga jami'an tsaro ko mazauna yankin.
Ya ƙara da cewa an ƙara tura jami'an tsaro zuwa yankin tare da ci gaba da sintiri domin tabbatar da zaman lafiya da kwantar da hankalin al'umma da kuma farautar waɗanda suka tsere.
A cewarsa, rundunar 'yan sanda ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyin al'umma, tare da kira ga jama'a da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da ayyukan ta'addanci.
Wannan lamari ya zo ne kasa da sa'o'i 24 bayan da jami'an tsaro suka dakile wani hari na 'yan bindiga a hanyar Gadar Manya da ke Ƙaramar Hukumar Anka, bayan fafatawar da ta ɗauki kusan sa'o'i biyu.
Hukumomi sun tabbatar wa mazauna yankunan cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin kawar da miyagun laifuka da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment