Har Fitsarin mu sai da muka sha domin mu tsira da rayuwarmu a yankin hamada - Inji wata Mata da ta dawo daga ƙasar Libya cirani.

Har Fitsarin mu sai da muka sha domin mu tsira da rayuwarmu a yankin hamada  - Inji wata Mata da ta dawo daga ƙasar Libya cirani.

Wata Mata ‘yar Najeriya mai shekaru 23 da ta dawo cirani daga ƙasar Libya, Endurance Daniel, ta bayyana irin wahalar da ta sha yayin ƙoƙarin hijira, inda ta ce ita da wasu ‘yan cirani har fitsari suka sha domin tsira da rayuwarsu a cikin hamadar Sahara saboda ƙarancin ruwa mai tsanani.

A cikin wata hira da aka yi da ita bayan dawowarta Najeriya ƙarƙashin taimakon Hukumar Ƙasa da Ƙasa kan Hijira (IOM), Daniel ta ce ta yi tafiya zuwa Libya tare da wasu ‘yan cirani su 52 a cikin mota guda. A cewarta, mutane bakwai sun rasu a hanya sakamakon tsananin wahala.

Daniel ta bayyana cewa an yaudare ta ne ta tafi Libya tun tana da shekara 17, inda aka yi mata alƙawarin aikin yi da rayuwa mai kyau. Wani abokin iyalinta ne ya rinjayi mahaifiyarta cewa za ta iya samun kuɗi cikin ɗan lokaci ta taimaki iyalinta.

“Mun shafe fiye da wata guda a hamada ba tare da ruwa ba. Don mu tsira, muna sha fitsarinmu. Daga baya wasu ba su ƙara iya fitsari ba, wasu ma jini ke fita daga jikinsu,” in ji ta.

Ta ce gawarwakin waɗanda suka mutu sun kasance a wurin har na kwanaki saboda babu yadda za a binne su ko ci gaba da tafiya.

Bayan isowarta Libya a shekarar 2019, Daniel ta gano cewa abin da aka yi mata alƙawari ya bambanta sosai da gaskiya. Ta ce mai daukar nauyinta ya gaya mata cewa mata ‘yan cirani suna da aikin gida ko kuma karuwanci kawai.

“Lokacin da na nemi in koma gida, aka ce sai na fara biyan kuɗin tafiya,” in ji ta, inda ta ƙara da cewa masu safarar mutane suna hana su amfani da waya domin kada su tuntuɓi iyalansu.

Daniel ta kuma zargi masu safarar mutane da amfani da barazana da tsoratarwa don tilasta wa ‘yan cirani yin abin da ba sa so, tare da yi musu barazanar sayar da su zuwa wuraren tilasta karuwanci idan suka ƙi.

Ta bayyana cewa ‘yan cirani suna fuskantar yunwa da mummunan yanayi a sansanonin wucin gadi, inda ake ba su abinci marar isasshen gina jiki.

Ta kuma ce ana ɓoye su a cikin motoci ana jigilar su a asirce domin guje wa jami’an tsaro da na shige da fice.

Duk da wannan wahala, Daniel ta nuna godiya bisa damar da ta samu ta komawa gida Najeriya. Ta shawarci matasa su tabbatar da sahihancin duk wani damar aiki kafin su shiga tafiyar haɗari zuwa ƙasashen waje.

“Bai kamata mutane su yarda da duk abin da aka faɗa musu ba. Abin da na fuskanta ya bambanta sosai da alkawuran da aka yi mini kafin in tafi,” in ji ta.

Labarinta na nuna irin haɗarin da ke tattare da hijira ta barauniyar hanya da kuma yadda ake cin zarafin ‘yan cirani yayin neman rayuwa mai kyau a ƙasashen waje. :::

0 $type={blogger}: