Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce Allah ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Matawalle ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa, yayin da ake samun ƙarin hare-haren ta’addanci da kisan gilla da kuma sace-sacen mutane a sassa daban-daban na ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu makarantu a Jihar Oyo, inda suka sace ɗalibai da malamai, yayin da wani hari a Jihar Borno ya haifar da sace ɗalibai da dama.
Ministan ya ce matsalar tsaro a Najeriya babbar ƙalubale ce ta ƙasa wadda ke bukatar haɗin kan hukumomin tsaro da gwamnati da kuma ‘yan ƙasa.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa jami’an tsaro baya tare da yin addu’a domin samun zaman lafiya, sannan ya yi gargaɗi kan amfani da batun tsaro wajen siyasa.
Matawalle ya zargi wasu ‘yan siyasa da yaɗa tsofaffin bidiyoyi a kafafen sada zumunta domin ɓata suna da nuna cewa gwamnati na gazawa.
Ya ce hukumomin tsaro na ci gaba da aiki tuƙuru wajen yaƙar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewarsa, matsalar tsaro ba ta Najeriya kaɗai ba ce, domin hatta manyan ƙasashe ma suna fuskantar irin wannan ƙalubale.
Ya ƙara da cewa duk da ƙoƙarin gwamnati, ba za a iya kawo ƙarshen matsalar cikin gaggawa ba, sai da haɗin kai da kuma ci gaba da goyon bayan ‘yan ƙasa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment