Aƙalla sojojin Indiya biyar ne suka mutu Sakamakon hatsarin Jirgin Sama a indiya.

Aƙalla sojojin Indiya biyar ne suka mutu Sakamakon  hatsarin Jirgin Sama a indiya.

Akalla jami’an Sojin Sama na Indiya (IAF) biyar ne suka rasu bayan wani jirgin dakon kaya na sojin sama ya yi hatsari a jihar Assam da ke arewa maso gabashin ƙasar.

A cewar rundunar sojin saman, jirgin samfurin Antonov An-32 ya yi hatsarin ne a kusa da yankin Jorhat yayin da yake gudanar da wani aikin horo na yau da kullum a ranar Asabar.

Rundunar ta tabbatar da cewa duka jami’an biyar da ke cikin jirgin sun mutu sakamakon hatsarin.

Sojin saman sun bayyana cewa an tura jami’an ceto da bincike zuwa wurin da hatsarin ya faru, yayin da aka fara bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.

Hotunan da kafafen yaɗa labarai suka nuna daga wurin hatsarin sun bayyana yadda hayaƙi mai kauri ya tashi daga tarkacen jirgin, wanda ya tarwatse zuwa sassa da dama bayan ya faɗi.

Sojin saman Indiya na amfani da jiragen An-32 sama da 100 wajen jigilar jami’ai da kayayyakin aiki a sassa daban-daban na ƙasar.

Wannan hatsari ya tunatar da wani makamancinsa da ya faru a shekarar 2019 a jihar Arunachal Pradesh kusa da iyakar China, inda mutane 13 suka mutu bayan wani jirgin An-32 ya yi hatsari.

Hukumomi sun ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto da tattara bayanai yayin da masu bincike ke ƙoƙarin gano ainihin abin da ya haddasa hatsarin.

0 $type={blogger}: