Tsohon Kakakin Rundunar Soji Janar Rabe Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Kakakin Rundunar Soji Janar Rabe Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Manjo Janar mai ritaya, Rabe Abubakar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ’yan bindiga.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Muazu, ya fitar a ranar Asabar, gwamnatin ta bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga Jihar Katsina da kuma Najeriya baki ɗaya.

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane. Ta ƙara da cewa gwamnati da jami’an tsaro sun yi ƙoƙari matuƙa wajen ganin an kuɓutar da shi cikin koshin lafiya, amma hakan bai yi nasara ba.

Gwamnatin ta bayyana cewa mutuwar Janar Rabe babban rashi ne ga iyalansa da Jihar Katsina da kuma ƙasa baki ɗaya. 
Ta kuma nuna cewa lamarin ya sake jaddada buƙatar ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar ’yan bindiga da rashin tsaro.

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, yana mai bayyana abin da ya faru a matsayin wani lokaci mai matuƙar baƙin ciki ga jihar. 
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗa kai da Gwamnatin Tarayya da  tsaro domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga tare da hukunta masu hannu a wannan aika-aika.

An sace Janar Rabe tare da matarsa a ranar 30 ga Mayu yayin da suke tafiya a cikin Jihar Katsina. Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun buƙaci a saki wasu mayaƙa uku da ake tsare da su tare da mayar musu da dabbobin da suka ce an kwace musu a yayin ayyukan tsaro kafin su saki ma’auratan.

Gwamnatin Jihar Katsina ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin tare da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

0 $type={blogger}: