Akalla Falasdinawa 11 suka rasa rayukansu, ciki har da mata yara kanana, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon jerin hare-haren jiragen saman Isra’ila a birnin Gaza a ranar Alhamis, Kamar yadda jami’an lafiya dake Gaza suka bayyana.
Mazauna yankin sun bayyana cewa jiragen sama na Isra’ila sun kai hare-hare ne a kan gine-ginen gidaje guda huɗu a yankunan Sheikh Radwan da Tel al-Hawa, da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Shati.
Hare-haren sun haddasa manyan fashe-fashe tare da lalata gine-gine da dama.
Bidiyoyi da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna mutane suna ƙoƙarin tserewa daga ginin da ke cin wuta a yankin Shati, yayin da hayaniya da tashin hankali suka mamaye wurin.
Sojojin Isra’ila sun ce farmakin ya nufi manyan shugabannin sashen tsaron cikin gida na Hamas ne. Inda suka bayyana cewa daga cikin wadanda aka kashe har da mataimakin shugaba Hassan Labad, da wasu mutune uku: Asim Shubair, Abdullah Abu Kaloub, da Mohammed Abu Marq.
Majiyoyi a Gaza sun ce Labad ya mutu ne tare da matarsa da ‘ya’yansa uku. Hukumar tsaron fararen hula ta Gaza kuma ta ce cikin wadanda suka mutu har da yara biyu masu nakasa daga iyalan Labad, da kuma mata uku.
Duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta shiga tsakani wacce aka fara a watan Oktoba 2025, Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare, Inda take zargin Hamas da sake gina ƙarfin sojinta.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce sama da mutane 940 suka mutu tun bayan fara yarjejeniyar.
Halin jinƙai a Gaza na ci gaba da tabarbarewa, yayin da ake gargadin ƙarin matsalolin jinƙai sakamakon ci gaba da rikicin.
Rahotanni kuma sun nuna cewa Isra’ila na shirin ƙara faɗaɗa yankin da take iko da shi a Gaza.
Rikicin ya fara ne tun bayan harin da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba 2023, inda hukumomin Isra’ila suka ce mutane kusan 1,200 suka mutu sannan aka yi garkuwa da 251. Isra’ila ta mayar da martani da babban farmakin soji a Gaza, wanda rahotanni daga ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce yayi sanadin mutuwar sama da mutane 72,950.

0 $type={blogger}:
Post a Comment