Shugaban Hukumar Zaɓen ƙasar Koriya ta Kudu Ya Yi Murabus Bayan an samu Karancin Takardun Zaɓe.

Shugaban Hukumar Zaɓen ƙasar Koriya ta Kudu Ya Yi Murabus Bayan an samu Karancin Takardun Zaɓe.

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasar Koriya ta Kudu, Roh Tae-ak, ya yi murabus bayan fuskantar suka mai yawa kan ƙarancin takardun zaɓe da ya haddasa tangarɗa a zaɓukan ƙananan hukumomi da aka gudanar kwanan nan a ƙasar.

Roh ya sanar da murabus ɗinsa a yau Juma’a, yana mai cewa ya ɗauki alhakin gazawar da ta faru wajen gudanar da zaɓen, wadda ta rage amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.

Ya bayyana cewa babu wata hujja da za ta kare matsalolin da suka hana wasu masu jefa ƙuri’a yin zaɓensu cikin sauƙi, tare da alƙawarin amincewa da sakamakon binciken da za a gudanar.

Shugaban mai murabus ɗin ya kuma sanar da kafa wani kwamitin ƙwararru masu zaman kansu domin binciken musabbabin matsalar da ta faru yayin zaɓen.

Matsalar ta fara ne bayan takardun zaɓe sun ƙare a kusan rumfunan zaɓe 50 a faɗin ƙasar, lamarin da ya tilasta jami’an zaɓe tura ƙarin takardu cikin gaggawa zuwa wuraren da abin ya shafa. 
Haka kuma, an samu jinkiri a wasu rumfunan zaɓe 22 sakamakon matsalolin sufuri da rarraba kayan zaɓe.

Koriya ta Kudu na gudanar da zaɓe ta hanyar amfani da kusan rumfunan zaɓe 14,300 a duk faɗin ƙasar, amma wannan ƙaranci ya haifar da ruɗani da fusatan masu zaɓe a wurare da dama.

A wasu cibiyoyin zaɓe, an ruwaito cewa masu jefa ƙuri’a sun shafe sa’o’i suna jira bayan lokacin rufe zaɓe na ƙarfe 6:00 na yamma.

Daya daga cikin wuraren da matsalar ta fi kamari shi ne gundumar Songpa da ke birnin Seoul, inda wasu fusatattun masu zaɓe suka hana jami’an zaɓe ɗaukar akwatunan ƙuri’u bayan kammala zaɓen.

Lamarin ya ci gaba har zuwa safiyar Juma’a kafin jami’an ‘yan sanda su shiga tsakani. 
An tura daruruwan jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro da kuma bai wa jami’an zaɓe damar kammala aikin kirga ƙuri’u.

Jami’an hukumar zaɓen sun bayyana cewa an buga takardun zaɓe ne bisa hasashen cewa mutane da dama za su yi amfani da damar kaɗa ƙuri’a kafin ranar zaɓe. Sai dai adadin masu fitowa zaɓen ya zarce yadda aka yi tsammani a wasu yankuna.

Duk da matsalolin da aka fuskanta, yawan masu kaɗa ƙuri’a ya kai kashi 63 cikin 100 a zaɓen da aka gudanar domin zaɓar gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi, da wakilan majalisun yankuna.

Lamarin ya jawo cece-kuce a ƙasar, inda wasu ‘yan ƙasa suka shigar da ƙorafe-ƙorafe ga hukumomi tare da neman kotun tsarin mulki ta ƙasar ta binciki ko an tauye musu haƙƙinsu na zaɓe.

Wannan rikici ya ƙara jawo hankalin jama’a kan yadda ake gudanar da zaɓe a Koriya ta Kudu tare da tayar da tambayoyi game da shirye-shiryen da hukumomin zaɓe ke yi kafin gudanar da manyan zaɓuka.

0 $type={blogger}: