‘Yan ta’adda sun kashe jami’an ‘yan sanda uku a Jihar Kwara

‘Yan ta’adda sun kashe jami’an ‘yan sanda uku a Jihar Kwara.

Wasu ‘yan ta’adda sun sake kai hari a kauyen Tenibo da ke karamar hukumar Kaiama a Jihar Kwara, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda uku na rundunar mobile police.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki 11 bayan da aka kashe sojoji uku a kauyen Kemanji bayan fafatawar bindiga da ta dauki sama da sa’o’i biyu.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya jefa tsoro da firgici a yankin Tenibo da makwabtan kauyuka, inda mazauna yankin ke fara kaura daga gidajensu zuwa wurare mafi aminci.

An ce harin na baya-bayan nan ya faru ne da tsakar dare, lokacin da ‘yan ta’addan suka fito daga cikin daji suka kai hari sansanin jami’an tsaron, inda suka bindige jami’an ‘yan sanda uku har lahira. Bayan harin, sun tsere suka koma cikin daji.

Wani ma’aikacin karamar hukumar Kaiama da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin. Haka kuma wani mazaunin yankin ya bukaci gwamnati da ta share dazukan da ‘yan ta’addan ke buya a ciki domin kawo karshen hare-haren.

Ya ce kusancin dajin da ke kusa da kauyen yana ba ‘yan ta’addan damar kai hare-hare cikin sauki sannan su koma buya. 
Ya kara da cewa idan gwamnati ta dauki mataki ta kori ‘yan ta’addan tare da ba manoma damar noma a yankin, hakan zai taimaka wajen dakile hare-haren.

Shugaban karamar hukumar Kaiama, Alhaji Abubakar Danladi, ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce gwamnati na kokarin hada kai da gwamnatin jiha da na tarayya domin kawo karshen irin wannan matsala.

Ya ce ba karamar hukuma kadai za ta iya shawo kan lamarin ba, don haka ana bukatar hadin gwiwa daga dukkan bangarorin domin tabbatar da tsaro a yankin.

0 $type={blogger}: