Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APM a hukumance, lamarin da ake ganin zai sauya yanayin siyasar jihar kafin babban zaɓen ƙasa na shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Asabar a Fadar Gwamnati da ke Bauchi, inda ya bayyana tare da Shugaban Jam’iyyar APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, da manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a siyasa.
Bala Mohammed ya ce matakin da ya ɗauka na sauya jam’iyya ya biyo bayan dogon nazari da tattaunawa da abokan siyasa da shugabanni a fadin jihar.
Ya bayyana matakin a matsayin mai muhimmanci domin ƙarfafa tubalinsa na siyasa da kuma samar wa magoya bayansa ingantacciyar hanya a gabanin zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa zama a cikin PDP ba zai ba shi damar haɗa kan magoya baya da cimma manufofinsa ba, don haka ya ga dacewar komawa wata jam’iyya da za ta ba shi dama mafi kyau.
Duk da haka, gwamnan ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar PDP bisa rawar da ta taka wajen bunƙasa siyasarsa, musamman wajen ba shi dama ya zama gwamna a shekarar 2019 da kuma matsayinsa a cikin jam’iyyar.
A yayin taron, Shugaban APM, Yusuf Dantalle, ya karɓi gwamnan a hukumance, inda ya ba shi katin zama ɗan jam’iyya tare da alamomin jam’iyyar.
Ana sa ran wannan sauyin jam’iyya zai yi tasiri sosai a siyasar jihar da ma ƙasa baki ɗaya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

0 $type={blogger}:
Post a Comment