Hukumomin Iran sun aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyu da aka samu da laifin yi wa hukumar leken asirin Israi'la, Mossad aiki.
An bayyana sunayen mutanen da Yaghoub Karimpour da Nasser Bekrzadeh, inda aka kashe su a lardin yammacin Azerbaijan da ke arewa maso yammacin ƙasar, bayan kotun koli ta tabbatar da hukuncin da aka yanke musu.
Rahotannin shari’a sun nuna cewa Karimpour ya kasance yana hulɗa da wani jami’in Mossad a lokacin rikicin shekarar 2025 tsakanin Iran da Israel tare da Amurka.
Ana zargin ya rika bai wa jami’in bayanai masu muhimmanci game da wurare da mutane domin karɓar kuɗi ta hanyar cryptocurrency.
Hukumomi sun kuma ce ya samu horo kan ƙera na’urorin fashewa, inda ake zargin ya ƙera su tare da amfani da su a wasu wurare, sannan ya aika hotuna da bidiyo ga wanda yake hulɗa da shi.
Bugu da ƙari, ana zargin ya ɗauki hotunan sansanonin soja da wasu muhimman wurare, tare da ɗaukar wasu mutane aiki domin aikata ayyukan ta’addanci, ciki har da ƙona na’urorin ATM a biranen Karaj da Mashhad.
Shi kuwa Bekrzadeh, an ce ya tattara hotuna da bayanai daga muhimman wurare a ƙasar, ciki har da cibiyar nukiliya ta Natanz, tare da aika bayanai kan wasu jami’ai da malamai.
An same su da laifuffuka da suka haɗa da “yaƙi da Allah” da kuma “lalata ƙasa” a ƙarƙashin dokokin ƙasar.
Hukumomin Iran sun ce sun kama mutane da dama da ake zargi da haɗa kai da hukumomin leken asiri na ƙasashen waje tun bayan rikicin shekaran 2025, tare da umartar kotuna da su gaggauta yanke hukunci kan irin waɗannan shari’o’i.

0 $type={blogger}:
Post a Comment