An Kama ’Yan Najeriya Biyu a Indiya Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

An Kama ’Yan Najeriya Biyu a Indiya Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

An kama wasu ’yan Najeriya biyu a ƙasar Indiya bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi, kamar yadda hukumomin tsaro suka bayyana.

Rahotanni sun nuna cewa an cafke mutanen ne a yankin Maidan Garhi da ke Kudancin Delhi bayan jami’an ’yan sanda sun samu sahihan bayanan sirri a ranar 27 ga Afrilu cewa wasu mutane za su iso yankin domin kai miyagun ƙwayoyi.

Jami’an tsaro sun shirya tarko tare da sanya ido, inda suka dakile waɗanda ake zargin da misalin ƙarfe 10:30 na dare yayin da suke kan babur (scooter).

Bayan bincike, jami’ai sun gano gram 102 na hodar iblis (cocaine) wanda ake ɗauka a matsayin adadi mai yawa, tare da gram 13 na MDMA da kuma gram 85 na methaqualone, wanda ke cikin matsakaicin adadi.

An bayyana sunayen waɗanda ake zargin da Chijioke Wisdom mai shekaru 26 daga Legas, da kuma Chiqozie mai shekaru 43 daga Owerri a Jihar Imo.

Hukumomi sun kuma ce mutanen biyu na zaune a Indiya ba tare da ingantattun takardun izini ba. An buɗe shari’a a kansu ƙarƙashin dokokin hana safarar miyagun ƙwayoyi, yayin da bincike ke ci gaba domin gano sauran masu hannu a lamarin da kuma hanyar samuwar ƙwayoyin.

0 $type={blogger}: