Rahotonnin sun bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na fuskantar rarrabuwar kai kan yanke shawarar wanda zai zama ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaben 2027.
Bayan hukuncin Kotun Koli da ya ba jam’iyyar wani ɗan sassauci na tsayawa takara, shugabannin ADC sun fara tattaunawa kan yadda za su warware sabani tsakanin manyan ‘yan siyasa masu sha’awar tikitin jam’iyyar.
Daga cikin sunayen da ake tattaunawa akai akwai tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Peter Obi da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan jam’iyyar sun kasu kashi biyu; wasu na goyon bayan tikitin Obi da Kwankwaso, yayin da wasu ke ganin Atiku zai iya haɗa kai da wasu ‘yan siyasa kamar Gwamna Seyi Makinde ko Amaechi.
Sai dai har yanzu ba a cimma matsaya ba kan wanda zai zama ɗan takara.
Masana siyasa sun yi gargadin cewa idan ADC ta kasa daidaita wannan rikici na cikin gida, hakan na iya rage mata ƙarfi a babban zaɓen 2027.

0 $type={blogger}:
Post a Comment