’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Jami’ai 17 A Harin Ta’addanci A Makarantar Sojoji a jihar Yobe.

’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Jami’ai 17 A Harin Ta’addanci A Makarantar Sojoji a jihar Yobe.

Rundunar'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’an ‘yan sanda 17 bayan wani harin ta’addanci da aka kai wata cibiyar horas da sojoji a garin Buni Yadi dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar lahadi, inda jami’an ke karbar horo na musamman kan yaki da ta’addanci da dabarun tsaro.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Anthony Placid, ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 1:15 na dare daga bangarori daban-daban.

An kuma ruwaito cewa wasu jami’an soji sun rasa rayukansu yayin da suke kokarin dakile harin.

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya bayyana mamatan a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare tsaron kasa. 
Ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da jaddada cewa ba za a manta da sadaukarwarsu ba.

Bayan harin, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Yobe, Usman Jibrin, ya ziyarci cibiyar horaswar domin jajanta wa jami’an soja da wadanda suka tsira daga harin.

Ya kuma bukaci jami’an da ke ci gaba da horo su kasance masu jajircewa tare da kammala shirin horaswar domin girmama abokan aikinsu da suka rasu.

Rundunar ‘yan sanda ta ce tana ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro domin gano maharan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

0 $type={blogger}: