Wani babban jami’in gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Shehu Yahaya Jalam, ya rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Marigayin, wanda shi ne Sakataren Dindindin na Musamman a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, ya rasu ne da safiyar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya.
Jalam, wanda ke riƙe da sarautar Turakin Dawakin Misau, yana cikin tawagar alhazan jihar Bauchi da suka je Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji lokacin da rashin lafiyar ta kama shi.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa Gwamna Bala Mohammed shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar da ma’aikatan gwamnati.
Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin jami’i mai ƙwazo da biyayya da jajircewa wajen gudanar da ayyukansa, musamman wajen shirya harkokin aikin Hajji da sauran ayyukan gwamnati.
Gwamnatin ta ce rasuwarsa babban gibi ne ga iyalansa da abokan aikinsa da kuma al’ummar jihar Bauchi baki ɗaya.
An gudanar da sallar jana’izarsa a ranar Lahadi bayan sallar Azahar a Masallacin Harami da ke Makkah.
Gwamna Bala Mohammed ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da abokan aiki da ma’aikatan gwamnatin jihar, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa Ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus.

0 $type={blogger}:
Post a Comment